A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Tarabulus fadar mulkin kasar Libiya a jiya Alhamis; Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka William Joseph Burns ya yi furuci da cewa; ‘yan ta’adda da masu dauke da tsaurin ra’ayin addini suna barazana ga zaman lafiyan kasar Libiya da ma duniya baki daya, tare da jaddada aniyar gwamnatin Amurka na gudanar da aiki kafada da kafada da kasar Libiya a fagen yaki da ta’addanci da nufin tabbatar da tsaro da bunkasa harkar tattalin arzikin kasar.
William Burns ya kara da cewar al’ummar Libiya suna sane da tarin matsalolin da kasarsu ke fuskanta amma har haka suna da damar daukan matakan shawo kan matsalolin.
Duk da kasancewar Amurka a matsayin sahun gaba a fagen goyon bayan ta’addanci a duniya musamman tallafawa ‘yan ta’adda da makamai da kudade kamar yadda take yi a halin yanzu haka a kasar Siriya amma ta kai ga yin furuci da rikidewar kasar Libiya zuwa tungar ‘yan ta’adda.ABNA